Isa ga babban shafi

Dole ECOWAS ta sake nazartar alakarta da kasashen yammaci - Tunis

Kakakin Majalisar gudanarwar kungiyar ECOWAS Sidie Tunis ya ce kungiyar na bukatar sake nazartar alakar da ke tsakaninta da kasashen yammaci bayan jerin juyin mulkin da kasashe mambobin kungiyar suka fuskanta.

Taron kungiyar ECOWAS a birnin Accra na Ghana.
Taron kungiyar ECOWAS a birnin Accra na Ghana. © Francis Kokoroko / Reuters
Talla

Juyin mulki da ya faru a kasashen na yammacin Afrika dai ya fito da baraka tsakanin mambobin kungiyar ta ECOWAS inda aka samu rarrabuwar kai musamman game da daukar mataki kan Nijar kasa ta baya-bayan nan da juyin mulkin ya faru.

A wata zantawarsa da jaridar Najeriya Premium Times, shugaban Majalisar ta ECOWAS Mr Tunis, ya bayyana cewa abubuwan da suka biyo bayan juyin mulkin Sojoji a Nijar sun bayyana yadda kasashen yammaci har zuwa yanzu ke nuna karfin iko da kuma yiwa harkokin kasashen Afrika karan tsaye musamman wadanda suka yi wa mulkin mallaka.

A ranar 26 ga watan Agusta ne jami’an tsaron fadar shugaban kasa a Nijar karkashin jagorancin Abdourahamane Tchiani suka hambarar da gwamnatin shugaba Bazoum Mohamed lamarin da ya haddasa rarrabuwar kai tsakanin kasashen ECOWAS dangane da matakin da za a dauka kan masu juyin mulkin.

Mr Tunis ya ce ya zama dole ECOWAS ta sake nazartar alakarta da kasashen na yammaci musamman tsakanin Faransa da kasashen da ta yi wa juyin mulki, lura da yadda tsana da kin jini ke ci gaba da zafafa tsakanin bangarorin biyu.

Kakakin Majalisar ta ECOWAS ya bayyana cewa idan har alaka tsakanin Faransa da kasashen da ta yi wa mulkin mallaka ta ci gaba da kasancewa a yadda ta ke yanzu, ko shakka babu yammacin Afrika zai ci gaba da ganin tarin matsaloli.

Bayan tabarbarewar alaka tsakanin Faransar da kasashen Mali da Burkina Faso, lamarin ya fi tsananta a Nijar inda a yanzu haka ake dambarwa kan yadda Paris za ta janye dakarunta dubu 1 da 500 da ke cikin Yamai, bayan tsanantar zanga-zangar 'yan kasar da ke neman ficewar ilahirin Faransawan da ke kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.