Isa ga babban shafi

Sojojin da suka kifar da gwamnatin Nijar sun ce za su tattauna da ECOWAS

Jagororin sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun ce a shirye suke  su tattaunawa don warware rikicinsu da ECOWAS, kamar yadda tawagar malaman addinin Musuluncin da ta ziyarci kasar ta bayyana a Lahadi bayan ganawarsu.

Janar Abdourahmane  Tiani, jagoran juyin mulkin Nijar.
Janar Abdourahmane Tiani, jagoran juyin mulkin Nijar. © RTN
Talla

Ziyarar tawagar malaman na zuwa ne a daidai lokacin da ECOWAS nazari a kan jerin zabin da take da shi don maido da maido da gwamnatin dimokaradiyya a Nijar, ciki har da amfani da karfi, biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli.

A wanni al’amari da ke alamta cewa ECOWAS na neman warware wannan rikici cikin ruwan sanyi, shugaban Najeriya da ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu ya amince da ziyarar malan a ranar Asabar, bayan da suka sha alwashin  tabbatar da ganin an sulhunta rikicin cikin ruwan sanyi.

A wata sanar a Lahadin nan, Sheikh Bala Lau, wanda ya jagoranci tawagar malaman, ya ce tawagar ta shafe tsawon sa’o’i tana tattaunawa da jagoran juyin mulkin Nijar din, Janar Abdourahamane Tiani, wanda ya ce kofarsa a bude take don warware rikicin ta hanyar diflomasiyya.

Gabanin ganawa da jagoran gwamnatin sojin Nijar, sai da tawagar malaman ta gana da firaministan da sojoji suka nada, Ali Mahaman Lamine Zeine a ranar Asabaar, duk a kokarin ganin an samo masalaha a rikicin siyasar kasar.

 

Wata majiya ta kusa da malaman ta ce tawagar  malaman ta shaida wa jagororin juyin mulkin Nijar cewa matakan da aka dauka a kansu daga ECOWAS ne, ba daga Najeriya ba, kamar yadda was uke tunani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.