Sojojin Nijar sun yi barazanar kashe Bazoum idan aka kai musu farmaki
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun yi barazanar kashe hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum idan har kasashen makwabta suka yi yunkurin amfani da karfin Soji don dawo da shi kan karagar mulki.
Wallafawa ranar:
Wasu manyan jami’an kasashen yamma 2 sun tabbatar da matsayar sojojin na Nijar ga kamfanin dillancin labarai na AP.
A cewar majiyoyin, Sojojin sun shaidawa karamar sakatariyar wajen Amurka Victoria Nuland a ziyarar da ta kai Nijar cikin makon nan cewa tabbas za su kashe Bazoum idan har wata kasa ta tasamma kai musu hari.
Kamfanin na AP ya ruwaito cewa hatta guda cikin jami’an Amurka ya tabbatar da wannan batu.
Bazoum wanda sojoji suka hambarar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan jiya, ya bayyana cewa ana ci gaba da tsare shi a cikin gidansa da ke fadar shugaban kasa, inda koka da nau’in abincin da Sojojin ke ciyar da shi.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyar ECOWAS ta umarci dakarunta su kasance cikin shirin kai hari kasar ta Nijar don tabbatar da dawowar mulkin Demokradiyya a kasar ta yammacin Afrika.
Yayin taron shugabannin kasashen kungiyar da ya gudana a Abuja jiya Alhamis, dukkaninsu su tafi akan matsayin matsa lamba ga sojojin na Nijar don tabbatar da dawowar mulkin farar hula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu