Isa ga babban shafi

Rukunin karshe na dakarun Faransa sun kammala ficewa daga Nijar

Rukunin karshe na Sojojin Faransa sun kammala ficewa daga Jamhuriyar Nijar wanda ke kawo karshen zaman fiye da shekaru 10 da dakarun suka yi a kasar ta yammacin Afrika don taimakawa wajen yakar ayyukan ta’addanci a Sahel.

Motocin Sojin Faransa yayin ficewa daga Nijar.
Motocin Sojin Faransa yayin ficewa daga Nijar. AFP - -
Talla

Gwamnatin Sojin Nijar da kanta ta tabbatar da kammala ficewar dakarun wanda ke biyo bayan juyin mulkin watan Yulin da ya gabata wanda ya kawo karshen huldar kasashen biyu.

Dakarun na Faransa sun fice ne bayan barin daruruwan takwarorinsu na Amurka da wasu gommai daga Jamus da Italiya a cikin kasar wadda ke karkashin ikon soji.

Laftanal Salim Ibrahim guda cikin jagororin mulkin sojin na Nijar ne ya sanar da kammala ficewar dakarun wanda ya ce, hakan ya kawo karshen kawancen tsaron kasar da Faransa wadda ta yi mata juyin mulki.

Faransa da kanta ta ce za ta janye ilahirin dakarun nata kusan dubu 1 da 500 daga Nijar bayan bukatar hakan daga sojojin da suka kwace mulki bayan hambarar da gwamnatin Bazoum Mohamed a ranar 26 ga watan Yuli.

Cikin kasa da watanni 18 dakarun na Faransa sun fuskanci kora daga kasashen Sahel 3 wadanda dukkaninsu Sojoji ke mulki da suka kunshi Mali da Burkina Faso da kuma Nijar.

Dukkanin kasashen 3 na fama da matsalolin tsaro daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi tun daga shekarar 2012.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.