Isa ga babban shafi

Lokaci ya yi da za mu kwaci cikakken 'yancinmu daga Faransa-Tchiani

Shugaban gwamnatin sojin Nijar Abdurrahmane Tchiani ya dorawa Faransa alhakin matsalolin da kasar ke fama da su tun bayan karbar juyin mulki, yayin da ya jadadda  tabbatar da tsaro da kuma fatattakar ta’addanci ko ta halin kaka.

Shugaban gwamnatin sojin Nijar Tchiani
Shugaban gwamnatin sojin Nijar Tchiani AP
Talla

Yayin da ya ke zantawa da manema a birnin Yamai Janar Tchiani ya ce yanzu haka kasar na kulla alaka da wasu kasashe don cimma burin ta, kuma nan ba da jimawa ba gwamnatin zata ci gaba da bibiyar tsaffin yarjejeniyoyin da Nijar din ta kulla da Faransa don yi musu gyaran fuska ko kuma kawo karshen su dungurungum.

Janar Tchiani ya ce a yanzu babban burin sa shine samar da sauki a tsakanin jama’ar kasar.

 

Mun gurzu a hannun Faransa don haka tura ta kai bango, inji Janar Tchiani.

Yayin tattaunawa Janar Tchiani ya ce matukar duniya zata kawar da son zuciya da siyasa to kuwa tabbas zata ga irin musgunawa da cin zafarin da Faransa ta rika yiwa Nijar don haka lokaci yayi da zamu kwaci cikakken ‘yancin ko ta halin kaka.

Ya ce nan gaba kadan Nijar zata ci gaba da daukar matakan da zasu fitar da ita daga kangin da wasu kasashen yammacin duniya suka jefata da sunan raino.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.