Isa ga babban shafi

Dubban 'yan Nijar na bikin murnar ficewar Jakadan Faransa daga kasar

Bayanai daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar na cewa dubban mutane sun taru gaban ofishin jakadancin Faransa don nuna farin cinki da ficewar jakadan Faransa daga kasar.

'Yan Nijar masu zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Faransa da ke birnin Yamai.
'Yan Nijar masu zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Faransa da ke birnin Yamai. © AFP
Talla

Duk da sanar da ficewar jakadan, masu fafutukar ganin Faransa ta fice daga kasar na ganin har yanzu tsugune bata kare ba.

A cewar masu wannan fafutuka, ficewar jakadan ba  shi ne karshen yakin ba, abinda ake bukatar samu shine cikakken ‘yancin Nijar, da rashin katsalandan daga Faransa ta kowacce fuska, tare da ci gaba da matsa lamba har sai kafatanin sojojin ta sun fice daga kasar baki daya.

A yanzu babban abinda jama’ar Nijar ke jira shine ganin Faransa ta fara janye sojojin ta sama da 1,500 sannu a hankali daga kasar kafin karshen shekarar da muke ciki.

Da farko dai Faransa ta bukaci tattara kafatanin sojojin ta dake Nijar a Yamai kafin su fara ficewa, sai dai sojojin da ke jagorantar kasar na ganin hakan hadari ne gare su, inda suka dage kan cewa sai dai sojojin su fice sannu a hankali.

Sojojin Faransar dai sun dade suna aiki da sunan yaki da ta’addanci a Nijar abinda al’ummar kasar ke ganin zamansu bai kara komai ba, illa ta’azzara ta’adddanci da suke ikirarin yaka.

Duk da wannan dambarwa dai gwamnatin sojin ta sanar da bayyana aniyar ta na sake dai-daitawa a kuma gyara alaka tsakanin kasar da Faransa a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.