Isa ga babban shafi

Rukunin farko na dakarun Faransa za su fara ficewa daga Nijar a yau Alhamis

A yau Alhamis, dakarun Faransa za su fara aikin janyewa daga Jamhuriyar Nijar, kamar dai yadda shugaba Emmanuel Macron ya alkawarta a ranar 24 ga watan Satumbar da ya gabata. 

Wani bangare na Sojin Faransa da ke shirin ficewa daga Nijar.
Wani bangare na Sojin Faransa da ke shirin ficewa daga Nijar. © THOMAS COEX / AFP
Talla

Sojojin Faransa na farko da za su fara ficewa a yau su ne dakaru 400 da ke a yankin Walam, daf da iyakar Nijar da Mali, kuma sun kasance suna aikin samar da tsaro ne karkashin wani shiri da aka yi wa take Operation Almahaou, wanda babbar manufarsa ita ce samar da tsaro a yankin Liptako. 

Wadannan dakaru za su isa birnin Yamai ne ta kasa, amma hakan na bukatar cikakken tsari da kuma tsaro ga ayarin sojojin daga inda za su tashi har zuwa cikin birnin Yamai.  

Duk da cewa tazarar ba ta wuce kilomita dari daya ba, amma dakarun za su iya share tsawon yini biyu saboda rashin kyawun hanya.

Da zarar sun isa Yamai kuwa, nan take dakarun 400 za su fara tashi zuwa Faransa ta jirgin sama.  

Rundunar sojojin Faransa dai ta ce tana fatan gudanar da wannan aiki ne da hadin-gwiwar mahukuntan Nijar, yayin da sojoji da suka kwaci mulki a kasar ke cewa ga alama Faransa ba ta da niyyar janye dakarunta daga kasar. 

Wannan dai gagarumin aiki ne da ya tanadi kwashe sojoji fiye da dubu daya da kuma manyan sundukai makare da kayan aikinsu, kuma dole sai an yi amfani da hanyoyi na kasa domin jigilar wadannan kaya a cikin watanni uku.  

To sai dai yayin da ake hasashen cewa za a isar da kayan ne a tashar jiragen ruwan birnin Cotonou, tuni mahukuntan sojin Nijar suka ce ba za su bude iyakar kasar ta bangaren jamhuriyar Benin ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.