Isa ga babban shafi

Amurka ta dawo da aikin sintirin jiragen yakinta a Nijar bayan juyin mulki

Shugaban rundunar sojin Amurka da ke kula da Turai da Afirka, Janar James Hecker, ya ce sun ci gaba da gudanar da sintiri da jiragensu na sama marasa matuka da kuma sauran jiragen Soji a Nijar, wadanda a baya juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar ya tilasta dakatar da ayyukansu. 

Wani jirgin yakin Soji marar matuki a Nijar.
Wani jirgin yakin Soji marar matuki a Nijar. AP - Malaury Buis
Talla

Babban kwamandan na sojojin saman Amurka a Afirka da Turan ya ce ci gaba da aikin na su ya biyo bayan tattaunawar da suka yi da gwamnatin mulkin Sojin Nijar. 

Tun bayan juyin mulkin da Sojojin Nijar suka yi a watan Yuli, dakarun Amurka 1,100 da ke kasar suka kasance a killace a sansanoninsu. 

Sai dai a makon da ya gabata ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon, ta ce an sauya matsugunin wasu sojojin kasar daga sansaninsu da ke kusa da birnin Yamai, zuwa wani sansanin Sojin da ke Agadez. 

Amurka dai ta mayar da Nijar a matsayin babbar cibiyar sansanin Sojojinta da ta dorawa alhakin gudanar da sintiri ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka masu dauke da makamai, domin yaki da ‘yan ta’adda, wadanda a tsawon shekaru suka kwace yankuna, tare da kashe fararen hula da kuma kai hare-hare kan sojojin kasashen waje.

Ko a shekarar 2018, sai da wasu 'yan ta'adda da ke ikirarin biyayya ga kungiyar IS suka kashe Sojojin Amurka hudu, da wasu na Nijar hudu da kuma wani tafinta, a harin kwanton baunar da suka kai musu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.