Isa ga babban shafi

Amurka zata aika da jami'an ta wasu kasashen yammacin Africa

Guda daga cikin manyan jami’an Diplomasiyyar Amurka zata ziyarci wasu kasashen yammacin Africa a kokarin da ake yin a kawo matsalolin da suka biyo bayan juyin mulkin jamhuriyar Nijar. 

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden REUTERS - JONATHAN ERNST
Talla

 

Babbar jami’ar diplomasiyyar Amurka Uwargida Molly Phee zata kai ziyarar Najeriya, Ghana da kuma Chadi, inda zata tattauna da shugabannin da nufin lalub hanyoyin da za’a bi wajen mayar da diplomasiyya a jamhuriyar Nijar. 

Babbar jami’ar diplomasiyyar Amurka Uwargida Molly Phee
Babbar jami’ar diplomasiyyar Amurka Uwargida Molly Phee © Flickr

Duk a yayin ziyarar za kuma ta yi wata ganawa ta musamman da jami’an diplomaisyyar kasashen Benin, Ivory Coast, Senegal da kuma Togo, inda za’a tattauna kan rawar da kungiyar ECOWAS ta taka tun bayan juyin mulkin. 

A cewar sanarwar da fadaer shugaban Amurka ta fitar, Phee zata mayar da hankali wajen ganin sojojin sun saki hambararren shugaba Muhammed Bazoum da suke rike da shi har yanzu. 

Fadar White House
Fadar White House © AP / Carolyn Kaster

A ziyarar da Uwar gida Molly zata kai Chadi, zata tattauna da shugaban kan rikcin Sudan da kuma halin da ‘yan gudun hijirar da ke samun makafa a Chadin ke ciki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.