Isa ga babban shafi

Amurka ta sake gargadin kasashen Afrika kan hada kai da Wagner

Amurka ta sake jaddada gargadinta ga kasashen Afirka, kan abin da ta kira da hadarin da ke tattare da kulla alaka da sojojin haya na Wagner, bayan boren da suka yi wa shugaban Rasha Vladimir Putin a karshen mako.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. REUTERS - JONATHAN ERNST
Talla

Kakakin ma’aikatar kulada harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya ce, irin wadannan abubuwan ne dama tun can baya ya sanya suke ta jan hankalin kasashe akai, domin a cewar sa duk kasar da Wagner ta shiga sai ta lallaka mutane da lalata dukiya da dama.

Dakarun sojin hayan na Wagner na kara kafuwa a nahiyar Afirka, inda gwamnatin mulkin sojin Mali ta dauko hayar hayar su tare da mara wa Rasha baya ta fuskar difulomasiyya, bayan tabarbarewar dangantaka tsakanin ta da Faransa da ta yi mulkin mallaka.

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, a wani rahoto da ta fitar a watan da ya gabata, ta ce sojojin Wagner ne suka kashe akalla mutane 500 a garin Moura da ke tsakiyar kasar Mali a watan Maris din shekarar 2022.

Toh sai dai a wata ganawa da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce boren da sojojin hayan Wagner suka yi a kasar ba zai shafe aikinsu na samar da zaman lafiya a kasashen Mali da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Lavrov ya ce Tarayyar Turai da Faransa sun zare hannun su kan lamuran tsaron kasashen, wanda yanzu ya ke a hannun Rasha da sojojin Wagner.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.