Isa ga babban shafi

Sauya matsayar Putin kan Wagner ya ja masa raini

Sojojin haya na Wagner sun koma tungarsu a jiya Lahadi bayan shugaba Vladimir Putin na Rasha ya amince ya janye zargin cin amanar kasa da ake yi wa shugaban sojin na Wagner tare da neman mafaka a kasar Belarus.

Shugaban Rasha Vladimir Poutine da shugaban sojojin hayar Wagner Evguéni Prigojine.
Shugaban Rasha Vladimir Poutine da shugaban sojojin hayar Wagner Evguéni Prigojine. AFP - GAVRIIL GRIGOROV,SERGEI ILNITSKY
Talla

Tuni kasashen duniya suka fara yi wa Putin kallo wani mutun mai rauni biyo bayan takun-sakan da ya barke tsakaninsa da sojojin na Wagner.

Yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma ta goge barazanar da dakarun shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin suka yi na mamaye birnin Moscow, fadar gwamnatin Rasha, yayin da masharhata ke cewa, ko babu komai, tawayen da sojojin suka yi wa Putin ya bayyana rauninsa karara ga idon duniya, ba kamar yadda aka zace shi ba.

An dai ga yadda aka girke tarin dakaru masu yaki da ‘yan ta’adda a babban birnin na Moscow bayan da aka hangi Mista Prigozhin a cikin motarsa kirar SUV a Rostov-on-Dov biye da manyan motocin yaki makare da mayaka a bayansa.

Tuni wadannan dakarun suka kwace shalkwatan sojoji a Rostov-on-Don kafin daga bisani su fice, yayin da kuma ya rage musu kimanin kilomita 400 su isa cikin birnin Moscow a cewar rahotanni.

Shugaba Putin dai ya bayyana wannan dabi’ar ta dakarun Wagner a matsayin cin amanar kasa, yana mai alkawarin cewa, zai hukunta su sakamakon yadda suka kusan jefa Rasha cikin yakin basasa.

Sai dai daga bisani, Putin ya cimma yarjejeniya da shugaban na Wagner wadda ta hana faruwar rikicin tsaro mafi muni cikin gomman shekaru a Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.