Isa ga babban shafi

Za mu ci gaba da tattaunawa da Afrika kan rikicin Ukraine - Rasha

Fadar Kremlin ta ce Rasha za ta ci gaba da tattaunawa da tawagar kungiyar kasashen Afirka da ke neman shiga tsakanin rikicinta da Ukraine, musamman a lokacin taron shekara-shekara da Rasha ke gudanarwa da kasashen Afirka, wanda za a yi a wata mai zuwa. 

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin © AP / Alexei Danichev
Talla

A ranar Asabar din da ta gabata ne shugaba Vladimir Putin ya gana da tawagar shugabannin kasashen Afirka 7 a St Petersburg, gameda rikicin su da Ukraine. 

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov, ya shaida wa manema labarai cewar Rasha za ta ci gaba da tattaunawa da tawagar Afrika, domin akwai wasu shawarwari da suka gabatar masu muhimmanci, duk kuwa da cewar bai bayyana wadanda suka ki amincewa da su ba. 

Ita dai wannan tawaga ta shugabannin Afirka karkashin jagorancin Cyril Ramaphosa, ta gabatar wa kasashen Rasha da Ukraine shawarwari har guda 10, wadanda matukar aka aiwatar da su, za a samu zaman lafiya.  

Daga cikin shawarwarin har da gaggauta tsagaita wuta, da mutunta ‘yancin kowace kasa da bayar da damar yin amfani da tashoshin jiragen ruwan kasashen biyu domin fitar da abinci zuwa sassan duniya da kuma yin musayar fursunonin yaki.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.