Isa ga babban shafi

Amurka ta gargadi kamfanin Wagner na kasar Rasha kan juyin mulkin Nijar

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yayi gargadin cerwar rundunar tsaron Wagner ta kasar Rasha na amfani da huyin mulkin da akayi a Jamhuriyar Nijar wajen samun wurin zama kamar yadda suka yi a makociyar kasar ta Mali. 

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, kenan daga hagu, tare da hambararren shugaban Nijar Muhammad Bazoum.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, kenan daga hagu, tare da hambararren shugaban Nijar Muhammad Bazoum. AP - Boureima Hama
Talla

Dangane da zargin cewar ko Wagner ta taka rawa wajen juyin juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar, Blinken yace babu wata shaidar dake nuna haka, amma akwai fargabar cewar kungiyar na iya amfani da wannan damar da ta samu a kasar. 

Sakataren yace abin takaici duk inda kungiyar Wagner ta sanya kafa, banda kashe kashe da lalata wurare da kuma amfani da dama wajen samun biyan bukata babu abinda take yi. 

Rundunar tsaron Wagner ya zuwa wannan lokaci ta kulla yarjejeniyar aiki da kasashe da dama a nahiyar Afirka, cikin su harda Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, abinda ya sa gwamnatocin kasashen yammacin duniya ke zargin su da take hakkin Bil Adama. 

Kasar Mali wadda sojoji ke jagoranci na daga cikin wadanda suka rungumi Rasha ta harkokin diflomasiya lokacin barkewar yakin Ukraine wanda dakarun wagner ke taka rawa sosai. 

Wakilan Mali da Burkina Faso sun ziyarci Jamhuriyar Nijar domin bayyana goyan bayan su ga sojojin da suka yi juyin mulki. 

Jamhuriyar Nijar ta baiwa kasashen Amurka da Faransa wurare domin kafa sansanin sojojin dake yaki da ta’addanci a yankin Sahel.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.