Isa ga babban shafi

Amurka ta gana da sojojin da suka kifar da gwamnatin Nijar amma babu masalaha

Amurka ta gana da jagororin gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar a Litinin don lalubo yadda sojojin za su mika mulki ga gwamnatin farar hula da ta hambarar, bayan da  suka yi watsi da  wa’adin da kungiyar ECOWAS ta dibar musu.

Shugaban Amurka, Joe Biden.
Shugaban Amurka, Joe Biden. © 路透社图片
Talla

Shahararriyar jami’ar diflomasiyya, kuma mataimakkiyar sakataren harkokin wajen Amurka, Victoria Nuland, ta ce ta yi tattaunawa ta tsawon sa’o’i biyu da jagororin gwamnatin sojin Nijar, wadanda suka wancakalal da gwamnatin  farar hula ta Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

Da take bayani ga manema labarai bayan tattauawar,  Nuland ta bayyana  ganawar a matsayin ta keke-da- keke, mai cike da sarkakiya.

Ta ce ta mika wa jagororin juyin mulkin zabi da dama don samun masalaha tare da maido da dangantaka da Amurka, wadda ta bi sahun sauran kasashen yammacin Turai wajen yanke agajin da take ba Nijar.

Ta kara da cewa sojojin ba su amince da bukatar ta ta ganawa da sabon shugaban gwamnatin sojin Nijar, ko kuma shugaba Mohamed Bazoum da suke tsare da shi ba, sai dai ta  ce jami’an Amurka suna mu’ammala da Bazoum ta wayar tarho.

Nuland ta ce ta gana da Janar Moussa Salou Barmou, wanda aka nada a matsayin sabon babban hafsan sojin kasar, wanda ta ce a baya ya yi aiki sau da kafa da Amurka da Faransa a game da yakin da ake da ta’addanci a yankin Sahel.

Ta kuma ce ta gargadi Nijar a game da bin sahun Malli wajen dauko kamfanin sojin hayar Wagner.

Kungiyar ECOWAS mai mambobi  15 za ta gudanar da  wani taro a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja don sake nazari a kan matakin diflomasiyyar da za ta  dauka.

Wata majiya kusa da ECOWAS ta ce babu batunn daukar matakin soji a kan Nijar a nan kusa don maido da Bazoum, tana mai cewa ba ta yanke kauna a kan tattaunawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.