Isa ga babban shafi

Amurka ta dakatar da tallafin da take baiwa Nijar har sai an dawo da tsarin dimokuradiyya

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya sanar da dakatar da wasu shirye-shirye da su kunshi ba da agaji ga Nijar bayan hambarar da zababben shugaban kasar da majalisar soji ta yi.

Sakataren harkokin wajen Amurka kenan, Antony Blinken, daga hagu, tare da hambararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum.
Sakataren harkokin wajen Amurka kenan, Antony Blinken, daga hagu, tare da hambararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum. AP - Boureima Hama
Talla

A karshen makon da ya gabata ne Faransa ta dakatar da duk wani taimakon raya kasa da take baiwa Nijar bayan juyin mulkin da aka yiwa shugaba Mohamed Bazoum. Kungiyar Tarayyar Turai da wasu kasashe da dama ma sun dakatar da goyon bayansu.

Duk da haka, "za a ci gaba da taimakon agajin jin kai na ceton rai da abinci" kuma Amurka za ta ci gaba da gudanar da ayyukan diflomasiyya da tsaro don kare jami'anta a kasar, in ji shi.

Nijar na samun kusan dala biliyan biyu a duk shekara a matsayin taimakon raya kasa a hukumance, a cewar bankin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.