Isa ga babban shafi

Bazoum ya roki Amurka da kasashen duniya su kare demokradiyar Nijar

Hambarerren shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum, ya roki Amurka da sauran kasashen duniya da su maido da kasar kan turbar tsarin mulki ka da su bari juyin mulki da sojoji ke ikirari ya tabbata a kasar.

Shugaban sojin Nijar Janar Abdourahamane Tchiani da Hambarerren shugaban kasar Mohamed Bazoum.
Shugaban sojin Nijar Janar Abdourahamane Tchiani da Hambarerren shugaban kasar Mohamed Bazoum. © AP / AP - Ludovic Marin / Montage RFI
Talla

A wani makala da ya rubuta cikin jaridar Washington Post, Bazoum ya yi kira ga gwamnatin Amurka da daukacin al'ummar duniya da su taimaka wajen maido da tsarin mulkin, yana mai da muddun juyin mulki yi nasara to babu shakka zai yi mummunan tasiri ga jamhuriyar Nijar da yankin su da ma duniya baki daya.

Wannan kira dogon bayani na farko da shugaba Bazoum ya yi tun bayan da jami’an tsaron fadarsa suka tsare shi a ranar 26 ga watan Yuli tare da karbe mulkin Nijar.

Garkuwa

Yace yana rubutun ne a matsayin wanda aka yi garkuwa da shi.

"Nijer na fuskantar hari daga shugabannin mulkin soji...kuma ina daya daga cikin daruruwan 'yan kasar da aka tsare ba bisa ka'ida ba."

"Dole ne a kawo karshen juyin mulkin, kuma dole ne shugabannin soji su sako duk wanda suka kama ba bisa ka'ida ba," in ji shi.

Bazoum, wanda ya hau kan karagar mulki bayan zaben  shekarar 2021, ya ce kasarsa ta kasance cikin murmurewa a yankin da ke fama da masu tsattsauran ra'ayi da kuma mulkin soja.

"Nijar ta kasance tungar karshe na mutunta hakkin dan adam a yankin Sahel da ke fama da rikici a Afirka, tsakanin gwamnatotin 'yan kama-karya da suka mamaye wasu makwabtanmu," in ji shi.

Ya yi gargadin cewa makwabtan Nijar na kara gayyato ‘yan ta’addan Rasha masu aikata laifuka irin su Wagner domin cin zarafin jama’arsu da mutuncinsu.

Matattarar Boko Haram

Ya kara da cewa, kungiyoyin ta'addanci irin na Boko Haram, ba shakka za su yi amfani da damar rashin zaman lafiya a Nijar, wajen maida kasar wata turbar tsara hare hare zuwa makwabta tare da kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro da walwala a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.