Isa ga babban shafi

Biden ya yi kira ga sojojin Nijar da su gaggauta sakin shugaba Bazoum

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira ga sojoji da suka yi juyin Mulki a Nijar da su gaggauta sakin zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum tare da mutunta  dimokradiyyar kasar.

Shugaban Amurka Joe Biden yayin jawabi ga 'yan jaridu bayan ganawa da takwaransa na Finlad Saili Niinisto. 13/07/23
Shugaban Amurka Joe Biden yayin jawabi ga 'yan jaridu bayan ganawa da takwaransa na Finlad Saili Niinisto. 13/07/23 © 路透社图片
Talla

Biden ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa ga Nijar da ke bukin ciki shekaru 63 da samun ‘yan cin kai daga turawa, inda ya bukaci gaggauta sakin shugaba Bazoum da iyalansa.

"A cikin wannan mawuyacin lokaci, Amurka na tare da jama'ar Nijar don girmama dangantakarmu ta shekaru da dama da suka samo asali daga manufofin dimokuradiyya tare da goyon bayan gudanar da mulkin farar hula.”

Bazoum mai shekaru 63 a duniya, a makon da ya gabata ne masu tsaron sa suka hambarar da shi a wani juyin mulkin da Amurka da kasashen Turai da Majalisar Dinkin Duniya suka yi Allah wadai da shi.

“Al’ummar Nijar na da ‘yancin zabar shugabanninsu,” in ji Biden. "Sun bayyana ra'ayinsu ta hanyar zaɓe na gaskiya da adalci - kuma dole ne a mutunta hakan."

A shekarar 2021 ne Mohamed Bazoum ya dare karagar mulkin Nijar, bayan nasarar lashe zaben da ya zama na farko da farar hula ya mika mulki ga farar hula cikin lumana.

Ya karbi ragamar mulkin kasar da aka yi fama da juye-juyen mulki hudu tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.