Isa ga babban shafi

Tinubu ya kare matakan ECOWAS kan gwamnatin sojin Nijar

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kare matakan da yake dauka a matsayin sa na shugaban kungiyar ECOWAS domin ganin an mayar da mulkin fararen hula a Jamhuriyar Nijar ganin yadda mutane ke ta cacaka matsayin na sa dangane da kawar da zababbiyar gwamnati. 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kuma sabon shugaban kungiyar ECOWAS.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kuma sabon shugaban kungiyar ECOWAS. © Twitter/DOlusegun
Talla

Mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelela ya shaidawa manema labarai cewar, duk matakan da Tinubu ke dauka a matsayin sa na shugaban Najeriya da kuma ECOWAS basu saba da sharidodin da kungiyar ta kasashen yammacin Afirka ta amince da su ba. 

Ngelela yace sabanin yadda ake kokarin mayar da matsalar ta Nijar ta zama ta addini ko kuma kabila, lamarin ya saba da haka, domin kuwa kasashen da suke cikin ECOWAS na dauke da kabilu da kuma addinai daban daban. 

Jami’in yace shugaba Tinubu na tintibar mutanen da suka dace a ciki da wajen Najeriya, cikin su harda gwamnonin jihohin da suka yi iyaka Nijar domin ganin an samu fahimtar juna dangane da matsalar wadda ke zama babbar barazana ga yankin Afirka ta Yamma baki daya. 

Ngelela yace har yanzu babu wani matsayi da ECOWAS ta yanke dangane da matsalar ta Nijar, domin ana ci gaba da daukar matakan diflomasiya da zummar ganin ya haifar da ‘da mai ido, kuma idan hakan ya gaza shugabannin zasu dauki matakan da suka dace a koda yaushe. 

Jami’in ya bayyana cewar shugabannin kasashen Afirka zasu gudanar da wani taro ranar alhamis 10 ga watan nan domin nazari akan matakan da aka dauka ya zuwa wannan lokaci da kuma gabatar da rahotannin tintibar da ake ci gaba da yi akan matsalar ta Nijar. 

Yan Najeriya daga bangarori da dama na ci gaba da bayyana adawar su da duk wani matakin soji, inda suka bukaci ECOWAS ta rungumi hanyoyi diflomasiya da dama domin warware matsalar ta Nijar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.