Isa ga babban shafi

ECOWAS ta kakabawa Jamhuriyar Nijar sabbin takunkumai

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS karkashin jagorancin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ta sanya sabbin takunkumi kan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.

Bola Ahmed Tinubu, na biyu daga dama, wato shugaban kungiyar ECOWAS kenan, kuma shugaban Najeriya, bayan ganawa da shugabannin kasashe mambobin kungiyar ranar 30 ga Yuli, 2023.
Bola Ahmed Tinubu, na biyu daga dama, wato shugaban kungiyar ECOWAS kenan, kuma shugaban Najeriya, bayan ganawa da shugabannin kasashe mambobin kungiyar ranar 30 ga Yuli, 2023. AP - Chinedu Asadu
Talla

A baya dai kungiyar kasashen yankin ta bai wa gwamnatin Nijar wa'adin kwanaki bakwai da ta maido da shugaba Mohamed Bazoum kan mukaminsa ko kuma a sanya mata takunkumi, ciki har da yiwuwar daukar matakin soji.

Sai dai masu sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi kira ga kungiyar ECOWAS da su yi watsi da duk wani Shirin tsoma bakin kasar Nijar din.

Haka kuma ta yanke hulda da Najeriya, Togo, Faransa da Amurka, sannan gwamnatin sojin ta rufe sararin samaniyar Nijar har sai baba ta gani.

A karshen wa'adin, kungiyar ta shirya wani taro a ranar Alhamis domin duba halin da ake ciki a yankin yammacin Afirka.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a ranar Talata, mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngeale, ya ce an kara sanyawa wasu mutane da hukumomin da ke da alaka da gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar karin takunkumi.

Ko da yake bai yi cikakken bayani ba, amma ya ce an yi hakan ne ta hannun babban bankin Najeriya CBN.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.