Isa ga babban shafi

Muna nazarin amfani da diflomasiyya domin kawo karshen juyin mulkin Nijar - ECOWAS

Kwamitin tsaro na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS wanda ya kunshi hafsoshin soja na wasu kasashen yammacin Afirka a ranar Juma'a, ya ce za su yi amfani da tsarin diflomasiyya wajen shiga Tsakani a Jamhuriyar Nijar kan juyin mulkin mulkin soja a kasar.

Hafsoshin tsaron kungiyar ECOWAS kenan, yayin wani taro a Abujan Najeriya.
Hafsoshin tsaron kungiyar ECOWAS kenan, yayin wani taro a Abujan Najeriya. AP - Chinedu Asadu
Talla

Manyan hafsoshin tsaron kasashen Togo da Saliyo da Senegal da Najeriya da Ghana da Laberiya da Guinea Bissau da Gambia da Cote’Divoire da Cape Verde da kuma Jamhuriyar Benin sun bayyana haka a karshen taronsu na kwanaki biyu a jiya juma’a.

Taron wanda aka fara tun a ranar Larabar da ta gabata, wanda shugaban kungiyar ta ECOWAS a hedkwatar tsaro da ke Abuja, Janar Christopher Musa ya jagoranta, bayanai sun ce sojojin Mali da Nijar da Guinea da kuma Burkina Faso sun yi watsi da shi.

Da yake karanta sanarwar taron ga manema labarai, Janar Musa ya ce sun yanke shawarar kara zage damtse wajen yin cudanya da duk wani mai ruwa da tsaki, da kuma tabbatar da tattaunawa da yin shawarwari wajen tunkarar rikicin Jamhuriyar Nijar.

Ya ce an yi juyin mulki kimanin takwas zuwa tara da aka yi nasara a yammacin Afirka a cikin shekaru uku da suka gabata, inda ya ce dukkan mambobin kungiyar ta ECOWAS sun kasance shugabannin da aka zaba ta hanyar dimokradiyya kafin shekaru uku da suka wuce.

Musah ya ce, a 'yan kwanakin nan an bayyana barazanar da sojoji ke yi a yammacin Afirka, yana mai cewa dole ne a yi kokarin shawo kan lamarin kafin ya kasance abin zunde ga kasashen Afirka da ma duniya baki daya ba.

Ya ce taron na hafsan hafsoshin tsaron ya kasance ne bisa ka’idar da ta shafi tsarin magance rikice-rikice, sasantawa, wanzar da zaman lafiya da tsaro, wanda aka amince da shi a shekarar 1999 kuma dukkanin kasashe mambobin kungiyar suka rattaba hannu a kai a shekarar 2001.

“Don haka za mu yi nasara, amma diflomasiyyance, kuma kamar yadda muka fada, zabin amfani da karfin soja shine na karshe game da batun tattaunawar. Kuma idan za mu iya guje wa hakan, tattaunawa cikin lumana shine mafi sauki, amma dole ne mu yi Shirin ko ta kwana.

“Lokaci ya sake waiwayar ECOWAS da za ta nuna cewa ita kungiya ce mai ka’ida, mu kasashe ne masu Mulki bisa tsarin doka; ba za mu yarda a maye gurbin dokar da take amfani da tsarin dimokradiyya da barazana ba,”in ji Musa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.