Isa ga babban shafi

Shugaban mulkin sojin Nijar ya ki ganawa da tawagar ECOWAS

Tawagar ECOWAS ta bar Nijar ba tare da ganawa da shugaban mulkin sojan da ya kwace mulki a wani juyin mulki da aka yi, yayin da wa’adin da kungiyar ta yammacin Afirka ta baiwa sojoji na su maida mulki ga Mohamed Bazoum ke kawo jiki.

Shugaban majalisar soji ta Nijar Janar Abdourahmane Tiani da mukarrabansa.28/07/23
Shugaban majalisar soji ta Nijar Janar Abdourahmane Tiani da mukarrabansa.28/07/23 REUTERS - STRINGER
Talla

Tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta isa Yamai babban birnin kasar a ranar Alhamis sai dai ba ta kwana a can ba kamar yadda aka tsara tun farko, ba ta kuma samu ganin jagoran juyin mulkin Abdourahamane Tiani ko hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ba.

Tawaga

Tawagar dai ta kasance karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Abdulsalami Abubakar, kuma tun da farko an tsara zata gana da Tiani domin gabatar da bukatun ECOWAS kamar yadda fadar shugaban Najeriyar ta bayyana.

Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar na III da kuma tsohon shugaban Najeriya Abdulsalami Abubakar.
Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar na III da kuma tsohon shugaban Najeriya Abdulsalami Abubakar. © Photos AFP - Montage RFI

Najeriya mafi girma a yankin, ita ce ke rike da shugabancin kungiyar ta ECOWAS, wadda ta kakaba takunkumi kan Nijar a ranar Lahadin da ta gabata tare da baiwa shugabannin juyin mulki wa’adin mako guda su maido da Bazoum karagar Mulki.

Sassauci

Sai dai shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce kungiyar za ta yi iya kokarinta don ganin an warware rikicin cikin ruwan sanyi, ko da yake kungiyar ECOWAS ta ce za ta iya daukar matakin soji a matsayin matakin karshe idan sojoji suka nuna turjiya.

Yayin da gwamnatin mulkin Nijar ta yi gargadin cewa ita ma duk Wanda yace mata kule to zata ce cas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.