Isa ga babban shafi

Nijar ta rufe sararin samaniyarta a yayin da wa'adin ECOWAS ya cika

Jamhuriyar Nijar ta rufe sararin samaniyarta bisa fargabar yiwuwar kai mata farmaki, bayan da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar suka yi kunnen uwar shegu da wa’adin da kungiyar ECOWAS ta yammacin Afrika ta dibar musu na mayar da hambararren shugaba Mohamed Bazoum kan mukaminsa.

Janar Omar Tchiani dai ya kasance mai kula da masu gadin fadar shugaban kasa tun a shekara ta 2015 kuma ya kasance na hannun damar tsohon shugaban kasar Issoufou.
Janar Omar Tchiani dai ya kasance mai kula da masu gadin fadar shugaban kasa tun a shekara ta 2015 kuma ya kasance na hannun damar tsohon shugaban kasar Issoufou. © ActuNiger
Talla

A wata sanarwa da ta fitar jim kadan bayan cikar wa’adin, gwamnatin sojin Nijar ta ce duba da shirye-shiryen da kungiyar ECOWAS ke yi na amfani da karfin soji a kanta don tilasta mata mayar da gwamnatin dimokaradiyya, taa rufe sararin samaniyarta daga jiya Lahadi.

Sanarwar ta kara da cewa duk wani yunkuri na keta bbjire waw ana mataki da gwamnatin soji ta dauka zai gamu da  zazzafan martini daga sojin Nijar.

A makon da ya gabata ne ECOWAS  ta sanar da wannan wa’adi, tana mai umurtar manyan hafsoshin sojin da suka kifar da gwamnatin dimokaradiyya su gaggauta sauka daga kan kujerar shugabancin kasar.

A ranar 26 ga watan Yuli aka hambarar da gwamantin Bazoum, bayan da dakarun da ke tsaron lafiyarsa suka yi garkuwa  da shi.

A wata sanarwa ta dabam, sabuwar gwamnatin   Nijar din ta ce wasu kasashen tsakiyar Afrika biyu suna shirin aike wa da dakaru don shirin ko-ta-kwana idan har batun harin da za a kai wa Nijar ya zama gaskiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.