Isa ga babban shafi

ECOWAS ta aike da tawagar sansantawa Jamhuriyar Nijar

Ana Sanya ran isar tawagar kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO birnin Yamai a yau Laraba don duba yiwuwar sasanci tsakanin sojojin da suka yi juyin Mulki da kuma gwamnatin farar hula. 

Tutar kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS/CEDEAO
Tutar kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS/CEDEAO REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

Tun bayan faruwar Juyin mulkin a Larabar makon jiya, ake ta samun musayar yawu da barazana a tsakanin kasashen duniya da manyan kungiyoyi da kuma sojojin da suka yi juyin Mulki, to amma kafin ECOWAS ta dauki matakin soji zuwa wa’adin makon gudan da ta bai wa sojojin, ta dauki matakin sasanta rashin jituwar ta hanyar diplomasiyya. 

Har yanzu dai babu wani hasashen masana game da yadda wannan tattaunawa za ta kasance. 

Sai dai akwai yiwuwar tattaunawar ba za ta haifar da da mai ido ba, la’akari da yadda kowanne bangare ya tsaya kai da fata neman samun biyan bukatarsa, yayin da kasashen duniya suka ja daga kan marrawa bangaren da suke so baya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.