Isa ga babban shafi

Wa'adin ECOWAS: Gwamnatin sojin Nijar na ci gaba da fuskantar matsin lamba

Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar, na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga manyan kasashen duniya, kan ta mika mulki ga hambararren shugaban kasar, Muhammad Bazoum.

Taron hafsoshin tsaron kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS kenan a Abujan Najeriya.
Taron hafsoshin tsaron kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS kenan a Abujan Najeriya. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Sabuwar gwamnatin dai a yanzu haka ta nemi taimako daga kamfanin sojojin haya na kasar Rasha wato Wagner, a daidai lokacin da wa’adin da kungiyar ECOWAS ta dibar mke cika a yau Lahadi.

Daya daga cikin jagororin juyin mulkin Janar Salifou Mody ne ya gabatar da wannan bukata yayin da ya ziyarci makwabciyar kasar Mali.

Majalisar mulkin Jamhuriyar Nijar na fuskantar wa'adin ranar 6 ga watan Agusta da kungiyar kasashen yankin da aka fi sani da ECOWAS ta sanya, na sakin tare da maido da zababben shugaban kasar Mohammed Bazoum, wanda ya bayyana kansa a matsayin wanda aka yi garkuwa da shi.

Itama Faransa ta nuna goyon bayanta ga kungiyar ECOWAS na kawo karshen juyin mulkin da sojojin kasar suka yi.

Manyan hafsoshin tsaro na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, sun tsara wani shiri na daukar matakin soji matukar shugabannin juyin mulkin ba su maido da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum zuwa ranar Lahadi ba, lamarin da ke kara tada jijiyoyin wuya a yankin da ke fama da hare-haren masu tayar da kayar baya.

Jagoran juyin mulkin mai shekaru 59, Janar Abdourahamane Tiani, wanda ya samu horon soji a Faransa, ya ce gwamnatin mulkin sojan ba za ta ja da baya ba, har yanzu suna kan bakarsu na jan ragamar mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.