Isa ga babban shafi

Nijar ta kammala horar da tubabbun mayakan Boko Haram 40

Jamhuriyar Nijar ta sanar da kammala horar da tubabbun mayakan boko haram sama da 40 da aka sauya tunanin su da kuma koya musu sana’oi a karkashin wani shirin gwamnatin kasar.

Shugaba Bazoum Mohammed
Shugaba Bazoum Mohammed © Niger Presidency
Talla

Wani jami’in hukuma ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, tubabbun mayakan 42 suka samu horo kuma yanzu haka sun bar cibiyar horar da su da ke Goudoumaria a yankin Diffa litinin din da ta gabata.

Rahotanni sun ce kowanne guda daga cikin mutanen 42 ya karbi kayayyakin sana’ar da ya koya da suka hada da na gyarar mota ko babur ko dinki ko aikin kafinta da walda ko kuma kasuwanci.

Bayanai sun ce an kuma horar da su akan yadda za su rage tsatsauran ra’ayin addini tare da rantsuwa da Alkur’ani cewar ba za su sake daukar makamai domin tada hankali ba.

Kungiyoyin da ke alaka da Al Qaeda da IS sun dade suna kai munanan hare haren ta’addanci a Nijar inda suke kashe dubban rayuka a yammacin kasar, yayinda mayakan da ke alaka da boko haram da IS ke kai hare hare a kudu maso gabashin kasar.

Wadannan mutane 42 su ne kashi na 3 da suka samu irin wannan horo, bayan 386 da aka horar inji ministan cikin gida Adamou Souley.

Janar Mahamadou Abou Tarka da ke jagorancin Cibiyar ya bayyana cewar suna samun nasara a aikin da suke yi wanda ya kunshi shirya tattaunawa a tsakanina al’umma.

Shugaba Bazoum Mohamed dai ya sanar da aniyar sulhunta da kungiyoyin da ke tayar da hankali da kai hare-hare a sassan Nijar da nufin kawo karshen matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.