Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Mayakan Boko Haram sun yi wa farar hula 40 yankan rago a Borno

Mayakan Boko haram sun kashe fara hula 40 a karamar hukumar Kala Balge ta jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar Boko Haram su na ci gaba da ta'asa jifa - jifa duka da kassara ta da hukumomin najeriya suka ce sun yi.
Kungiyar Boko Haram su na ci gaba da ta'asa jifa - jifa duka da kassara ta da hukumomin najeriya suka ce sun yi. Youtube
Talla

Rahotanni sun ce dimbim ‘yan ta’adda ne suka yi wa farar hula da basu dauke da makami kawanya, inda suka yi ta yi musu yankan rago a ranar Lahadi.

‘Yar majalisar wakilai ta Tarayyar Najeriya da ke wakiltar mazabar, Zainab Gimba ta tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labari.

 Wata majiya ta tsaro ta shaida wa jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa  Najeriya ta ce an kashe  msu sana’ar gwangwan da dama, kuma tuni aka binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Wani rahoton kuma ya yi nuni da cewa gwamman ‘yan ta’adda ne suka kai wa farar hular, wadanda kananan manoma ne farmaki da takuba.

yanzu ana nan ana laluben sauran gawarwakin wadanda ba a gani ba a cikin dazukan da lamarin ya auku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.