Isa ga babban shafi

Sojan da ke taimaka wa Boko Haram ya kashe kansa

Wani sojin Najeriya da aka kama yana taimaka wa ‘yan ta’adda ya kashe kansa, sai dai har yanzu ba a fayyace ko jami’in sojin yana wa Boko Haram ko ISWAP ne aiki ba.

An zargi sojan da aiki tare da Boko Haram a jihar Yobe
An zargi sojan da aiki tare da Boko Haram a jihar Yobe © AFP/Reinnier Kaze
Talla

Sojan ya kashe kansa ne a yayin da ake tafiya da shi barikin soji don ya amsa tambayoyi a ranar Talata.

Asirinsa ya tonu ne ta wajen aikin da  jami’an sojin leken asiri suka gudanar, lamarin da ya bankado hannu da ya ke da shi a mummunan kisan da aka yi a wasu otel otel da gidajen barasa a jihar Yobe.

Sojan mai suna Lance Corporal Jibrin, wanda mai horar da jami’an soji ne a bataliyarsa a Geidam, ya shafe kwanaki  ba a ganshi ba, lamarin da ya sa aka shiga zarginsa da aikata ba daidai ba.

Daga bisani kuma aka ce an hango shi a cikin mayakan ISWAP da suka kai farmaki a garuruwan jihar Yobe.

Daga nan ne aka shiga bibiyarsa ta wayar hannunsa, inda aka fahimci yana garin  Gashua, kilkomita da dama daga ainihin inda yake aiki.

Bayan ya shiga hannu, rahotanni sun ce Jibrin, ya bayyana sunayen wasu sojoji da suke wannan danyen aiki tare, amma a kan hanyarsu ta komawa Geidam ya kwace bindiga daga wani abokin aiki ya kashe kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.