Isa ga babban shafi

'Yan gudun hijira fiye da dubu 36 sun shiga Nijar a bana - MDD

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, ta ce sabbin ‘yan gudun hijira fiye da 36,000 ne suka isa Nijar a tsakanin watan Janairu zuwa tsakiyar watan Afrilu sakamakon tashin hankalin da suka tserewa a kasashen Mali, da Najeriya da Burkina Faso.

Wasu 'yan kasar Mali da ke gudun hijira a Jamhuriyar Nijar.
Wasu 'yan kasar Mali da ke gudun hijira a Jamhuriyar Nijar. © UNHCR/H. Caux.
Talla

Karin sabbin ‘yan gudun hijirar ya sanya jumilar adadin wadanda tashe-tashen hankulan suka raba da muhallansu, wadanda kuma a yanzu ke samun mafaka a Nijar kaiwa kusan 360,000.

Wakilin hukumar UNHCR a Nijar Emmanuel Gignac ya bayyana fargabar cewa za a rika samun kwararar mutane akai-akai zuwa Nijar muddin aka cigaba da fuskantar matsalolin tsaro a kasashen da ke kewaye da kasar.

Hukumar UNHCR ta ce, sabbin bakin da suka fito daga kasar Mali na tserewa fadan da ake yi ne tsakanin kungiyar IS da ke yankin Sahara da kuma ‘yan tawayen kungiyar MSA da ke neman kafuwar kasar Azawad a arewacin Gao da Menaka.

Sansanin 'yan gudun hijira na Sinegodar da ke dauke da 'yan Mali kimanin 7000 a Jamhuriyar Nijar.
Sansanin 'yan gudun hijira na Sinegodar da ke dauke da 'yan Mali kimanin 7000 a Jamhuriyar Nijar. © OCHA/Nicole Lawrence

‘Yan gudun hijirar Najeriya kuwa na tserewa karuwar hare-haren da ‘yan bindiga ke yi ne a jihohin Katsina da Sokoto, a arewa maso yammacin kasar tasu, yayin da kuma gudun hijira daga Burkina Faso suka tsere daga kasar, suma saboda yaduwar matsalar rashin tsaro.

Wannan kalubale na zuwa ne a daidai lokacin da alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka nuna cewar kimanin mutane 580,000 da aka tilastawa yin gudun hijira, ciki har da baki 360,000 daga kasashe makwabta, ke zaune a Jamhuriyar Nijar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, halin da ake ciki a Nijar, musamman yankin yammacinta, ana fama da matsalar karancin abinci sakamakon fari da hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi da suka hana manoma yin noma.

Garuruwan Tahou da Tillaberi da ke kan yankin da ya hada iyakokin Burkina Faso, da Mali da ita kanta kasar ta Nijar na fuskantar munanan hare-haren mayaka masu alaka da kungiyoyin Al-Qaeda da IS, wadda ita ma ke da karfi a Mali da Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.