Isa ga babban shafi
Mali-Nijar- Hijira

Dubban mutane sun tsere zuwa Nijar sakamakon rikice-rikice a Mali

Dubban mutane ne suka isa Jamhuriyar Nijar bayan da suka tsere wa rikici da ake  yi tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a arewacin Mali, kamar yadda wani rahoton majalisar dinkin duniya ya bayyana a jiya Juma’a.

Taswirar Nijar da ke nuna Tillaberi.
Taswirar Nijar da ke nuna Tillaberi. AFP
Talla

Rahoton ya ce kusan mutane dubu 18 ne ‘yan kasar Mali da ma ‘ya Nijar da ke zaune a Mali suka gudu daga kauyukan Inchinana, Azaragane, Anderamboukane da Tamalet suka nemi mafaka a Tilleberi da Tahoua a yammacin Jamhuriyar Nijar.

Ofishin kula da ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniya ya ce sama da fararen hula 400 ne aka yi amannar sun mutu sakamakon rikicin na kungiyoyi masu dauke da makamai.

Wasu daga cikin ‘yan gudun hjirar na karbar taimako daga hukumar abinci ta duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.