Isa ga babban shafi
Nijar - Tillaberi

Nijar: rashin tsaro ya tilasta rufe daruruwan makarantu a Tillabéri

Hukumar kula da ayyukan  jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA, ta ce an rufe makarantu 580 a jihar Tillaberi da ke yammacin Jamhuriyar Nijar saboda matsalar tsaro, abin da ke nufin cewa kashi 24% na makarantun yankin sun daina aiki baki daya.

Taswirar garin Tillabéri a Nijar
Taswirar garin Tillabéri a Nijar © RFI
Talla

Shugaban ofishin hukumar ta OCHA a Nijar Modibo Traore, ya ce dalibai sama da dubu 53 ne suka daina zuwa makaranta a yankin, saboda yadda ‘yan bindiga ke yi wa malamai barazana da kuma yadda suke tserewa suna barin yankunan da matsalar ta shafa.

Modibo ya kara da cewar a shekarar bana kawai matsalar tsaron ta tilasta rufe karin makarantu fiye da 200 a yankin na Tillaberi.

Modibo Traore ya kuma bayyana cewa hukumomin Nijar sun tsara shirin bayar da agajin gaggawa na tsawon watanni uku masu zuwa, inda yayi kira ga masu hannu da shuni da su marawa kokarin gwamnati da abokan huldarta.

A cikin watan Mayun da ya gabata cikin shekarar 2021, an samu kwararar dimbin ‘yan gudun hijira daga kauyuka zuwa cikin garin Tillaberi da ke yammacin Jamhuriyar Nijar wadanda ke tserewa hare-haren ‘yan bindiga a kusa da iyakar kasar da Mali.

A waccan lokacin, gwamnan jihar ta Tillaberi Ibrahim Tijjani Katiella, ya tabbatar da cewa adadin ‘yan gudun hijirar ya zarce dubu 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.