Isa ga babban shafi
Nijar-MDD

MDD ta jinjina wa Nijar kan karbar 'yan gudun hijira

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta gamsu da hukumomin Jamhuriyar Nijar saboda yadda suka bai wa 'yan gudun hijira sama da dubu 240 mafaka a cikin kasar.

Wasu 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya, a sansanin Asanga dake gaf da garin Diffa a Jamhuriyar Nijar. 16/6/2016.
Wasu 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya, a sansanin Asanga dake gaf da garin Diffa a Jamhuriyar Nijar. 16/6/2016. © ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Mataimakin Babban Jami’in Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya Mamady Fatta Kourouma, ya bayyana gamsuwar bayan ganawarsa da shugaban Nijar Bazoum Mohamed a  yankin Bangui da ke jihar Madaoua.

Ya yi amfani da wannan dama domin isar da godiyar hukumar  da ke kula da ‘yan gudun hijira ga hukumomin na Nijar ,ganin hadin kan da amincewa na karbar wadanan 'yan gudun hijira.

Yankin Tahoua na daga cikin yankunan kasar da aka tare 'yan gudun hijira dubu 20, yayin da wasu dubu 15 ke neman izini don samun mafaka  a wurarren da aka shirya na karbar 'yan gudun hijira.

A karshe, jami’in da ke magana da sunan hukumar ta UNHCR ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da kawo na ta gudunmuwa ga al’umar kauyuka takwas da aka ware a matsayin sansanin 'yan gudun hijira dake kauyen Bangui na garin Madaoua, tare da daukar alkawalin kawo tarin goyan baya da taimako ga sauren kauyuka 26 da ke yankin Tillia na kasar ta Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.