Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar: 'Yan adawa sun bukaci shugaban kasa ya sauka

‘Yan adawa da kngiyoyin fararen hula a Jamhuriyyar Nijar sun fitar da wata takardar sanarwa, da a ciki suke buakatar shugaban kasar, Issoufou Mahamadou ya sauka daga mukaminsa.

Shugaban kasar Jamhuriyyar Nijar Issoufou Mahamadou
Shugaban kasar Jamhuriyyar Nijar Issoufou Mahamadou atlasinfo
Talla

Gamayyar kungiyoyin ‘yan adawar da fararen hular na zargin shugaban kasar da karya dokokin kasa, yada rasahawa da kuma nuna gazawa a cikin aikinsa.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ‘yan adawar ke bukatar shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa, tare da jaddada aniyarsu ta ci gaba da yin gwagwarmayar cimma burinsu.

Sai dai a zantawarsa da Sashin Hausa na RFI, Iro Sani, sakataren yada labaran jam’iyyar PNDS Tarayya da ke mulkin kasar, ya ce kalaman ‘yan adawar ba su da wani tasiri.

A cewar Iro Sani manufofi da kuma matakin da ‘yan adawar suka dauka sun yi hannun riga da turbar dimokaradiyya.

00:54

NIGER-POLITICS-IRO-SANI-2017-05-23

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.