Isa ga babban shafi

Yan majalisun arewacin Najeriya sun zargi Shugaban Majalisar da yi cushe

A Najeriya ,Yan majalisu masu wakilcin arewacin kasar a karkashin kungiyar Sanatocin Arewa (NSF) sun tunkari Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan zargi shugaban majalisar dattijai da sanya ayyukan da suka kai Naira Tiriliyan 4 a cikin kasafin kudin 2024.

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio kenan.
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio kenan. © PremiumTimes
Talla

 

Wakilan kungiyar mai wakilai 58 karkashin jagorancin shugabanta, Abdul Ningi (PDP, Bauchi), sun fuskanci Shugaban Majalisar Akpabio a wani taro da ya gudana ranar Alhamis a dakin taro da ke Abuja.

Mambobin majalisar dattawan da suka halarci taron mai cike da rudani, baya ga shugaban majalisar Akpabio, akwai mataimakinsa, Barau Jibrin (APC, Kano), da kuma babban mai shari'a, Ali Ndume (APC, Borno).

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio kenan.
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio kenan. © PremiumTimes

Sanatocin arewacin Najeriya sun kuma zargi shugaban majalisar da yi wa sanatocin layin dogo domin su yi gaggawar zartar da "kasafin kudin da ba a taba gani ba a tarihin Najeriya".

Sanata Godswill Akpabio sabon shugaban majalisar dattijan Najeriya.
Sanata Godswill Akpabio sabon shugaban majalisar dattijan Najeriya. © The Guardian Nigeria

Wasu daga cikin bayyanan da manema labarai suka samu na dada nuni cewa Shugaban Majalisar ba zai iya kare wannan zargi ba amma ya ce ayyukan da aka koka da su watakila wasu da ba a san ko su wanene ba ne suka shigar da su cikin kasafin kudin yayin da shi (shugaban majalisar dattawa) ke kwance a asibiti a lokacin da ake gudanar da kasafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.