A makwannin baya bayan nan an ga irin matakan da gwamnatin Najeriya musamman babban bankin kasar ke dauka don ceto darajar Naira da kuma daidaita tattalin arziki da zummar kawo karshen kuncin da ‘yan kasar ke ciki.
Daga cikin matakan da aka aiwatar din kuma akwai soke lasisi cibiyoyin canjin kudaden waje sama da dubu 4 A Najeriyar, baya sauya tsarin bayar lasisin kafa sabbin cibiyoyin, sai kuma kara yawan kudin ruwan da babban bankin kasar CBN yayi.
Dangane da wadannan matakai, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Kasim Kurfi masananin tattalin arziki a Najeriyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu