Isa ga babban shafi

'Yan gudun hijirar Najeriya 12 sun mutu a wani hatsarin mota a Kamaru

'Yan gudun hijirar Najeriya 12 ne suka mutu da suka hada da mace mai juna biyu da jarirai hudu, yayin da wasu 22 suka jikkata a wani hatsarin motar bas da ya afku a ranar Alhamis a kusa da Maroua a yankin Arewa mai Nisa na kasar Kamaru, in ji gwamnan yankin Bakari Midjiyawa.

Hatsarin mota
Hatsarin mota Tristan Savatier/Getty Images
Talla

 

Kimanin fasinjoji talatin, dukkan ‘yan gudun hijirar ‘yan asalin Najeriya  da kuma suka fito daga  Minawao a kan hanyar wajen karbar abincinsu na wata-wata,” in ji gwamnan karamar hukumar.

Motar da marigayin dan wasan tseren fanfalakin ya yi hatsari a cikinta.
Motar da marigayin dan wasan tseren fanfalakin ya yi hatsari a cikinta. REUTERS - STRINGER

Wasu alkaluma na dada nuni cewa karamar m,otar ta dauke fasinjoji fiye da kima ,banda haka ba ta da tayoyi masu kyau.

Sansanin Minawao mai tazarar kilomita 30 daga kan iyaka da Najeriya, na dauke da 'yan kasar sama da 76,000 da suka tsere daga rikicin jihadi wanda arewa maso gabashin kasar ke fama da shi tun shekara ta 2009, a cewar alkaluman Majalisar Dimkin Duniya.

Wani hatsarin mota a Senegal
Wani hatsarin mota a Senegal © Ousseynou Diop/AFP

Fiye da mutane 6,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a kan hanyoyin kasar Kamaru, ko kuma sama da 30 ke mutuwa a cikin 100,000 mazaunan, daya daga cikin mafi girma a Afirka, a cewar Bankin Duniya, da sabbin bayanai da aka samu daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da aka buga a ciki 2018.

Wannan alkalumman sun ninka bayanan da hukumomi suka bayar kan yawan mace-macen kan hanya sau bakwai. Bisa kididdigar da wani jami'in ma'aikatar sufurin kasar Kamaru ya buga a cikin wata rana ta kasa a watan Yunin 2022, mutane 963 ne suka mutu a hatsarin mota a shekarar 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.