Isa ga babban shafi

Najeriya: Gobara ta hallaka mutum uku a sansanin gudun hijar Maiduguri

Akalla wasu ‘yan gudun hijira uku sun mutu sannan sama da gidaje 1000 sun kone bayan da gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke Maiduguri na jihar Barno dake arewacin Najeriya.

Gobara ta lakume sansanin 'yan gudun hijar Muna dake Maiduguri na jihar Barno. 15/11/23
Gobara ta lakume sansanin 'yan gudun hijar Muna dake Maiduguri na jihar Barno. 15/11/23 © zulum
Talla

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safiyar Laraba kuma ta dauki sama da awa daya kafin jami’an kashe gobara su shawo kan ta.

Babban Darakta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, Dokta Barkindo Muhammad Sa'idu ne ya bayyana hakan a Maiduguri, inda ya ce mayakan sakai na CJTF, da jami’an tsaro da ma su kansu ‘yan gudun hijira, sun taimaka gaya wajen kashe gobarar.

Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron jami'an.

Muryar Mohammed Barkindo Sa'idu shugaban hukumar agaji na jihar Barno
01:05

NIGERIA-BORNO-FIRE-OUTBREAK-MOHAMMED-BARKINDO-2023-11-15

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.