Isa ga babban shafi

Zulum ya sake tsugunar da al'ummar Kirawa bayan shekaru 6 na gudun hijira

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi tattaki wannan Asabar zuwa garin Kirawa mai makwabtaka da kasar Kamaru a karamar hukumar Gwoza, inda ya sa ido kan yadda aka sake tsugunar da kimanin iyalai 2,500 da suka rasa matsugunansu saboda rikicin Boko Haram, inda yanzu gwamnatin jihar ta sake ginawa.

Gwamnan jihar Barno Farfesa Babagana Umara Zulum, yayin tsugunar al'ummar Kirawa dake karamar hukumar Gwoza. 11/06/22.
Gwamnan jihar Barno Farfesa Babagana Umara Zulum, yayin tsugunar al'ummar Kirawa dake karamar hukumar Gwoza. 11/06/22. © Govenment House Maiduguri
Talla

‘Yan Boko Haram suka lalata gidajen a lokacin da suke mamaya, lamarin da ya tilastawa mazauna garin zama ‘yan gudun hijira a garin Pulka da ke wani gari a Gwoza, yayin da wasu suka tsere makwabciyarsu Kamaru inda suka samun mafaka. Kirawa ya kasance babu kowa tsawon fiye da shekaru shida.

Rabon gidaje

Gwamna Zulum ya kafa wani kwamitin sake gina gidajen da aka lalata a garin Kirawa da kuma sake tsugunar da wadanda suke bukatar komawa gida.

Gwamna Zulum, ya yi tattaki garin Kirawa domin sake tsugunar da jama’a, tare da sa ido a kan rabon kudi har Naira miliyan 120 ga 2,500 da kuma kayayyakin abinci.

Magidanta sun samu Naira dubu 100 kowannensu, yayin da matansu suka karni Naira dubu 20.

Kayan abinci

Bugu da kari, dukkan magidanta 2,500 kowannen su ya samu kayan abinci da suka hada da buhun shinkafa, buhun garin masara da kuma atamfa ga mata.

Gwamna Babagana Zulum da ya koma Maidugu da  yammacin Asabar ya samu rakiyar shugaban kwamitin sake matsugunin Kirawa, Engr Saleh Vungas wanda ya fito daga Gwoza kuma shi ne tsohon kwamishinan gidaje da makamashi.

Tawagar ta kuma hada da dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltar karamar hukumar Gwoza, Abacha Buba, tsohon kwamishinan noma, Engr. Bukar Talba da sakataren din-din-din na ma'aikatar yaki da fatara da sauran jami'an gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.