Isa ga babban shafi

NEMA ta karbi 'yan ciranin Najeriya 144 da suka makale a jamhuriyyar Nijar

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta sanar da karbar rukunin farko na ‘yan ciranin kasar dauke da mutane 144 da suka makale a jamhuriyyar Nijar ko dai akan hanyar su ta zuwa kasashen duniya don ci rani ko kuma akan hanyarsu ta dawowa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da irin haka ke faruwa ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da irin haka ke faruwa ba. OCHA/Yasmina Guerda/REUTERS
Talla

Da tsakar ranar jiya litinin jirgin ‘yan ciranin ya sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano inda daraktan hukumar ta NEMA reshen jihar ya karbe su wadanda aka dakko su a jirgin saman kamfanin Sky Mali Airlines kirar B737-400.

Daraktan wanda shugaban sashen ayyukan jinkai na hukumar Suleiman Sa’ad-Abubakar ya wakilta a wajen klarbar ‘yan ciranin, ya ce sun isa jihar ta Kano ne bisa kulawar jami’an hukumar kula da ‘yan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya IOM karkashin shirin mayar da mutanen da suka makale a Niamey garuruwansu.

 

Wasu 'yan ci-ranin Nijar da suka koma gida daga Libya
Wasu daga cikin 'yan ci-ranin Nijar a Libya
Wasu daga cikin 'yan ci-ranin Nijar a Libya REUTERS/Ismail Zitouny

Mr Abdullahi ya ce mutanen 144 sun hada da maza 106 sai mata 16 da kuma yara kanana 22, wanda bayanai ke cewa sun fito ne daga jihohin Kano da Kaduna da Katsina da Abia da kuma Sokoto da Edo.

Rahotanni sun ce galibi 'yan ciranin na Najeriya kan ratsa Jamhuriyyar Nijar ne don isa ko dai kasashen Algeria da Libya ko kuma bi ta ruwa su je Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.