Isa ga babban shafi

Yau kotun daukaka kara zata yanke hukuncin zaben gwamnan Filato

Najeriya – Yau ake saran kotun daukaka kara dake Najeriya ta yanke hukunci a kan karar zaben gwamnan jihar Filato wanda jam’iyyar APC ta gabatar, inda take kalubalantar zaben gwamna Caleb Mutfwang na jam’iyyar PDP.

Gwamna Caleb Mutfwang
Gwamna Caleb Mutfwang © Punch Nigeria
Talla

Kotun ta sanar da bangarorin dake cikin shari’ar cewar da misalin karfe 12 na rana zata yanke hukuncin a Abuja, bayan ta kammala sauraron lauyoyin masu gabatar da kara da kuma wadanda ake karar.

Hukumar zabe ta kasa ta bayyana Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a watan Maris, amma sai jam’iyyar APC da ‘dan takaranta Nentawe Yilwatda Goshwe suka ruga kotu inda suke kalubalantar nasarar PDP da kuma zargin cewar bata da shugabancin da doka ta tanada wajen tsayar da ‘yan takara.

Alkalan da suka saurari karar a kotunan zabe, sun bai wa PDP nasara, amma sai APC da ‘dan takararta suka saukaka kara.

Jam’iyyar APC ta bukaci kotun daukaka karar da tayi amfani da hurumin ta wajen yin adalci a shari’ar wadda ke ci gaba da dauke hankalin jama’a a ciki da wajen jihar Filato.

Ya zuwa wannan lokaci, jam’iyyar PDP a jihar Filato tayi asarar kujerun da ta samu nasara na majalisar dattawa da na wakilai da kuma na jiha, saboda irin wannan zargi na rashin bin umarnin kotu da kuma rashin hurumin gabatar da ‘yan takara a zabubbukan da suka gabata.

Kotun zabe a jihar ta mikawa ‘yan takarar jam’iyyar APC da Labour kujerun PDP saboda kin bin umarnin kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.