NRC ta musanta zargin satar taragan jirgi da aka yi wa manbobinta a Borno
Cacar baka ta barke tsakanin gwamnatin Jihar Borno da kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen kasa ta Najeriya, bayan da ‘yan sanda suka kame wasu manbobinta a bisa zargin cewa barayi ne da suka yi yunkurin awon gaba da wasu taragan jirgin kasa.
Wallafawa ranar:
A ranar Asabar din da ta gabata ‘yan sandan jihar Borno suka cafke wasu jami’an hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya NRC bisa zarginsu da yunkurin sace taragan jirgin kasa.
Yayin bayyana bacin ransa kan lamarin Innocent Luka Ajiji shugaban kungiyar ma'aikatan na NRC, ya ce babu gaskiya kan tuhumar da ake yi wa manbobin nasu.
Shugaban kungiyar ma'aikatan kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya Innocent Luka Ajiji
Sai dai mataimakin gwamnan jihar Borno Umar Usman Kadafur, ya musanta zargin da kungiyar ma’aikatan jiragen kasan Najeriyar ke musu, inda ya kara da cewar, matakin hana daukar taragan jirgin kasan da suka dauka ya biyo bayan zanga-zangar da mutane suka yi kan adawa da kwashe taragan.
Matiamakin Gwamnan Jihar Borno Umar Usman Kadafur
Kungiyar ma’aikatan kula da sufurin jiragen kasan ta Najeriya dai ta yi gargadin cewa za ta dakatar da ayyukanta, muddin ba a gaggauta sakin ma’aikatan nata da aka kama ba bisa ka’ida ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu