Isa ga babban shafi

Mutane 3 sun mutu bayan taho-mu-gama tsakanin jirgin kasa da mota a Lagos

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Lagos ta tabbatar da mutuwar akalla mutane 3 baya ga wasu da dama da suka jikkata, a wani hadarin da aka yi tsakanin jirgin kasa da kuma babbar motar daukar ma’aikata ta BRT a yankin Sogunle na jihar Lagos.

Wani  jirgin kasa a  tashar jiragen kasa dake birnin Legas da ke tarayyar Najeriya.
Wani jirgin kasa a tashar jiragen kasa dake birnin Legas da ke tarayyar Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Rahotanni sun nuna cewar lamarin ya faru ne a lokacin da motar da ke dauke da ma’aikata ke kokarin ketara layin doga a yankin Ikeja Along na jihar.

Kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta kasar NEMA Ibrahim Farinloye, da ke tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami'ansu sun kai dauki wajen da hadarin ya faru kuma akwai tarin mutane da suka jikkata wadanda tuni aka mika su ga asibitoci don samun kulawar gaggawa.

Rahotannin sun bayyana cewa akwai yuwuwar adadin wadanda suka mutu a sanadiyyar hadarin jirgin kasan da ya taso daga garin Abeokuta na jihar Ogun zuwa Lagos ya karu lura da halin jigatuwar da mutanen da suka samu rauni suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.