Isa ga babban shafi
Pakistan

Mutane 17 sun mutu a hadarin jirgin kasa a Karachi

Mutane fiye da 17 ne yanzu haka aka tabbatar da mutuwar su, yayin da wasu da dama suka samu rauni a lokacin da wasu jiragen kasa guda biyu suka yi taho mu gama a birnin Karachi dake Pakistan.

Wani hadarin jirgin kasa da ya auku a Pakistan a watan Satumbar 2016.
Wani hadarin jirgin kasa da ya auku a Pakistan a watan Satumbar 2016. Reuters/路透社
Talla

Hotunan bidiyo sun nuna masu aikin agaji na ta kokarin ganin sun kai doki ga mutanen da tarugun jiragen suka danne.

Wani jami’in Yankin yace akalla fasinjoji 1,000 ke cikin jiragen biyu lokacin hadarin abinda yasa ake ganin alkaluman mamatan zai iya karuwa.

Kawo yanzu dai an dage zirga-zirgar jiragen kasa a sauran sassan kasar na wani lokaci.

Hadarin dai ya auku ne a safiyar yau alkhamis a lokacin da al'umma ke rige-rigen soma ayyukansu na yau da kullum.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.