Isa ga babban shafi
Pakistan

Jiragen kasa guda biyu sun yi karo da juna a Pakistan

Akalla mutane 4 aka tababtar da mutuwar su yayin da sama da 100 suka samu raunuka a kasar Pakistan lokacin da wasu jiragen kasa guda biyu suka yi taho mu gama yau da safe.

Jiragen Kasa Biyu sun yi karo a Pakistan
Jiragen Kasa Biyu sun yi karo a Pakistan REUTERS/Khalid Chaudry
Talla

Rahotanni sun ce an samu hadarin ne a garin Multan lokacin da jirgin daukar kaya ya yi karo da na daukar mutane.

Wani jami’in kula da sufurin jiragen Saima Bashir ya zargi direban jirgin da ke dauke da mutane da rashin lura da wutar da aka kunna dan ankarar da shi ya tsaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.