Isa ga babban shafi
Pakistan

An kashe masu aikin Polio a Pakistan

Mayakan Taliban sun kai hari tare da hallaka ‘yan sanda 7 dake aikin tsare jami’an lafiya a yayin da suke baiwa yara riga kafin Polio a birnin Karachi dake Pakistan.

Allura Polio
Allura Polio AFP PHOTO / GWENN DUBOURTHOUMIEU
Talla

A baya mayakan sun shahara wajen kai hari kan jami’an kiwon lafiya don adawar da suke da yaki da cutar Polio, sai dai kuma a baya bayanann mayakan Taliban sun koma kai harin akan jami’an tsaro dake aikin kare su.

Bayan aukuwar lamarin kungiyar Taliban reshen Pakistan ta dauki alhakin kai harin na yau.

Pakistan na daga cikin kasashen duniya da ake da yawan alkaluma na yara da cutar Polio ke hallakawa duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.