Isa ga babban shafi
Pakistan

Mutane 700 sun mutu saboda tsananin zafi a Pakistan

Mahukuntan Pakistan sun ce akalla mutane 700 suka mutu sakamakon yanayin tsananin zafi da aka shafe kwanaki uku ana fama da shi a kasar. Yanzu haka an kafa dokar ta-baci a Asibitocin kasar, bayan sun cika makil da marasa lafiya, musamman Asibitin birnin Karachi inda mutane da dama suka mutu.

Mutanen Pakistan na sanyaya jiki a bakin rafi saboda tsananin zafi
Mutanen Pakistan na sanyaya jiki a bakin rafi saboda tsananin zafi Reuters
Talla

Jami’an lafiya na ci gaba da kula da daruruwan marasa lafiya.

Jami’an na Lafiya sun ce kusan mutane 700 suka mutu, yayin da ma’aunin zafin ya kai maki 45 na Celsius.

Adadin mutanen da suka mutu sun fi yawa a Karachi, inda ake kula da lafiyar mutane sama da 3000.

An shafe kwanaki uku ana fama da yanayin zafi a Pakistan, kuma al’amarin na faruwa ne a yayin da al’ummar kasar miliyan 200 ke gudanar da Azumin watan Ramadan, inda ake takaita ci da sha daga fitowar Al fijr har zuwa faduwar rana.

Masana addinin Islama na ci gaba da gabatar da fatawa akan duk wanda zai tagayyara yana da damar ajiye Azuminsa.

Kungiyoyin agaji na ci gaba da samar da hanyoyin sanyaya jiki ga al’umma musamman saboda matsalar lantarki da ake fama da ita a cikin lokacin na yanayin Zafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.