‘Yan bindiga sun kashe mabiya Shi’a 43 a Pakistan
Wasu ‘Yan bindiga sun bude wa wata mota kirar Bus wuta da ke dauke da mabiya Shi’a tare da kashe mutane akalla 43 da raunana 13 a birnin Karachi na kasar Pakistan a yau Laraba. ‘Yan bindiga guda shida ne suka bude wa Motar wuta da karamar Bindiga bayan sun zo saman babura, kamar yadda ‘Yan sandan Pakistan suka tabbatar.
Wallafawa ranar:
An bayyana harin a matsayin mafi muni tun harin da aka kai a watan Janairu inda wani dan kunar bakin wake ya dala wa kansa Bom a wani masallaci da ke kudancin Shikapur tare da kashe mutane 61.
Pakistan dai na fama da matsalar rikicin babbancin akida, musamman akan mabiya shi’a tsiraru a kasar mai yawan musulmi Miliyan 200.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu