Isa ga babban shafi
Pakistan

Hadarin jirgin kasa ya hallaka sama da mutane 40 a Pakistan

A kasar Pakistan, akalla mutane 40 suka mutu sakamakon taho mugama da jiragen kasa biyu suka yi a yankin kudancin kasar.

Jiragen Kasa Biyu sun yi karo a Pakistan, shekarar 2016
Jiragen Kasa Biyu sun yi karo a Pakistan, shekarar 2016 REUTERS/Khalid Chaudry
Talla

Kafofin yada labaran kasar sun ce jiragen sun yi karo da juna ne a kusa da garin Daharki dake arewacin Yankin Sindh, inda masu aikin agaji na cigaba da kwashe wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti.

Wannan dai ba shine karon farko da kasar Pakistan ke fuskantar hadarin jiragen kasar ta ba, ko a watan Nuwambar 2016,  sama da mutane 17 sun mutu yayin da wasu da dama suka samu rauni a lokacin da wasu jiragen kasa guda biyu suka yi taho mu gama a birnin Karachi dake kasar ta Pakistan.

Hotunan bidiyo sun nuna masu aikin agaji na ta kokarin ganin sun kai dauki ga mutanen da tarugun jiragen suka danne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.