Isa ga babban shafi

Lagos ta kaddamar da jirgin kasa na zamani irinsa na farko

Gwamnatin jihar Lagos da ke Najeriya ta kaddamar da jirgin kasa mai amfani da wutar lantarki irinsa na zamani, inda kuma tuni ya yi jigilarsa ta farko a yau Litinin.

Gwamnan jihar Lagos Sanwo Olu tare da wasu fasinjojin jirgin kasan da aka kaddamar yau litinin.
Gwamnan jihar Lagos Sanwo Olu tare da wasu fasinjojin jirgin kasan da aka kaddamar yau litinin. © Lagos state government
Talla

Bayanai sun ce gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu shi ne fasinja na farko da ya fara shiga jirgin, jim kadan bayan kaddamar da shi daga unguwar Marina zuwa Mile12.

Kodayake jawabi yayin kaddamar da jirgin, gwamna Babajide ya ce gwamnatin jihar ta yanke kaso 50 cikin 100 na kudin sufurin jirgin ga wadanda suke da katin shiga.

Gwamnan ya kuma kara da cewa da samun wannan jirgi, al’ummar jihar Lagos suna da damar kewayawa duk inda suke so ba tare da shiga cunkoson ababen hawa da jihar ta yi kaurin suna a kai ba.

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu, yayin kaddamar da jirgin kasan
Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu, yayin kaddamar da jirgin kasan © Lagos state government

Bayanai sun nuna cewa, an tsara jirgin da cikakken tsaro, yayin da aka makala masa kyamarorin sirri fiye da 300 da kuma samar da sansanin jamia’n tsaro a duk tashar da zai tsaya don sauka ko kuma shigar fasinja.

Baya ga hana kuma an samar wa da jirgin cibiyar wutar lantarki tasa ta kansa don ci gaba da aiki ba tare da fargabar dauke wuta ba.

Ya ku jama’ar Lagos ku tuna wannan aiki na ku ne, don haka mu ci moriyarsa yadda ya kamata cikin girmamawa da alfahari, kasancewar gwamnatinmu ba za ta lamunci lalatawa ko kuma rashin alkinta jirgin da duk abinda ke cikin sa ba” inji gwamna Olu.

Tuni jama’ar Lagos suka fara rububin shiga jirgin duk da korafin da ake yi na tsadar kudin jigilar..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.