Isa ga babban shafi

An samu saukar farashin man jirgin sama da gas din girki a Najeriya

Rahotanni a Najeriya na nuna yadda aka samu saukar farashin man jirgi da kuma gas din girki wanda ke da nasaba da cire tallafin man fetur da sabuwar gwamnatin kasar ta yi.

Matakin dai na zuwa ne bayan cire tallafin man fetur a Najeriyar.
Matakin dai na zuwa ne bayan cire tallafin man fetur a Najeriyar. AFP - JEFF PACHOUD
Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriyar ta ruwaito cewa daga farashin Naira 800 da ake sayen man jirgi a baya daga ranar 1 ga watan Yuni farashin ya koma Naira 650 a Lagos kana 680 a Abuja, ko da ya ke akwai banbancin farashin a jihohin Kano da Maiduguri da kuma Port Harcourt.

Jaridar ta ce farashin na ci gaba da sauka a kusan kowacce rana tun bayan kamawar watan da muke ciki na Yuni inda a jiya aka sayar da man jirgin kan farashin Naira 620 a Lagos, 660 a Abuja kana 680 a Kano.

Kafin yanzu dai ana sayar da man jirgin a farashin Naira dubu guda duk lita guda, batun da wani mai sayar da man ke cewa baya rasa nasaba da karancin bukatar man daga masu saye.

A bangaren gas din girki wanda a baya ake cika tukunyar gas mai nauyin kilogiram 12.5 kan farashin dubu 14 yau a jihar Lagos an sayar da shi Naira dubu 6,950 sabanin yadda aka sayar da shi dubu 8 a jiya litinin.

Rahotanni sun ce yanzu haka farashin kowanne kilogiram na gas baya haura Naira dari 7 zuwa 800 a kusan dukkanin sassan Najeriya sabanin yadda aka rika sayenshi dubu guda a makwannin da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.