Isa ga babban shafi
Tattalin Arziki

Tsadar gas din girki na ta'azzara a Najeriya

Tsadar iskar gas da ake girki da shi a Najeriya na dada ta’azzara, inda ga dukkanin alamu an kusa kaiwa matakin da mutane da dama za su hakura da shi domin komawa hanyoyin girki na gargajiya wato wajen amfani da itace ko kuma gawayi.

Wasu 'yan Najeriya yayin layin neman sayen gas din girki.
Wasu 'yan Najeriya yayin layin neman sayen gas din girki. © Daily Trust
Talla

Wannan matsala ta taso ne a daidai lokacin da hukumomin kasa da kasa da kuma manyan kungiyoyi ke fafutukar kawo karshen amfani da makamashin dake gurbata yanayi da muhallin dan Adam.

Wakilinmu na Abuja Mohammed Sani Abubakar ya nazarci matsalar kamar yadda za a ji a cikin rahotonsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.